NLC ta gargadi shugaba Buhari
Kungiyoyin kwadago NLC da TUC a Najeriya sun gargadi gwamnatin kasar da ta janye karin kudin man Fetur da ta yi a makon da ya wuce.
Kungiyoyin sun ce talakawan Najeriya na cikin mawuyacin hali, dan haka bai kamata a kara musu wata wahalar da karin farashin man fetur ba daga Naira 87 zuwa 145.
Dan haka sun gargadi Shugaba Buhari da ya gaggauta maida tallafin mai da ya janye wanda shi ne ya janyo tashin farashin man.
Sun dai bada wa'adin ranar Talata 17 ga wannan watan, matukar abu wani mataki da gwamnati ta dauka, za su bazama yajin aiki na sai baba ta gani da ya hada da ma'aikatan gwamnati, da na Bankuna, da gidajen saida mai da sauran su.
NLC ta gargadi shugaba Buhari
Reviewed by Unknown
on
9:35:00 PM
Rating:
No comments: