ads

Na Yi Rantsuwar Da Babu Kaffara, PDP Ce Za Ta Lashe Zabukan 2019 —Lamido



An bayyana gazawar gwamnatin Muhammadu Buhari, musamman a fannin rashin tabuka wani abin a zo a gani a shekara daya da ta yi a bisa karagar mulki da cewa ya bayyana karara zaben shekara ta 2019, ‘yan Nijeriya za su dawo daga rakiyar jam’iyyar APC a kowane mataki.
Kalaman hakan sun fito ne daga bakin Tsohon Gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido a yayin da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan kammala taron zaben Shugabannin jam’iyyar PDP na yankin jihohin Arewa Maso Yamma, wanda suka hada da, Kaduna, Kano, Katsina, Kebbi, Jigawa, Sokoto, da kuma Jihar Zamfara, wanda ya gudana a dakin taro da ke kasuwar Duniya ta Kaduna.

Alhaji Sule Lamido ya kara da bayyana cewa, “yanzu dai dukkan ‘yan Nijeriya sun yarda kuma sun gamsu da cewa Buhari da jam’iyyarsa ta APC, mulkin Nijeriya ya fi karfin su, ba za su iya ba, sun yaudari talakawan Nijeriya, sun iza su sun gaza fidda su. Dama na riga na san da haka, shi ya sa na yi rantsuwar da ba zan yi mata kaffara ba cewa, jam’iyya mai adalci ta talakawa, ita ce Jam’iyyar PDP, kuma za ta dawo kan madafun iko a shekarar 2019 In sha Allah.”
Sule Lamido ya ci gaba da bayyana cewa, “kwarewa da iya Shugabanci yana wajen ‘ya’yan jam’iyyar PDP, fada da cikawa tana wajen jam’iyyar PDP, rayuwa cikin arziki da walwala, yana ga Shugabannin jam’iyyar PDP. Amma sai ga shi tun kafin tafiya ta yi nisa an yaudari al’ummar Nijeriya da rana tsaka, aka kwaso ‘yan cuwa-cuwa aka gabatar masu, suka saki reshe suka kama ganye. Sai ga shi tun ba a je ko’ina ba jama’a suna kuka, wanda wannan shi ne sakamakon wanda ya yi butulci ga ni’imar Ubangijinsa.” In ji Sule Lamido.
Shi ma a yayin da yake jawabi, Tsohon Gwamnan jihar Kogi, Alhaji Idris Wada, wanda kuma shi ne ya jagoranci sanya ido akan yadda aka gudanar da zaben Shugabanin Jam’iyyar PDP na shiyyar, ya bayyyana cewa Jam’iyyar PDP ce kawai jam’iyya daya tilo wacce ta dace da al’ummar kasar nan, kuma za ta kai jama’a ga tudun mun-tsira, ba Jam’iyyar ‘yan nanaye ba.”
Ambasada Ibrahim Kazaure ne aka zaba a matsayin Shugaban jam’iyyar PDP na yankin Arewa maso Yamma, ya yi rantsuwar ganin ya dawo da dukkan kujerun da jam’iyyar PDP ta rasa a shiyyar ga ‘ya’yanta a zabuka masu zuwa nan gaba cikin gaggawa.
Na Yi Rantsuwar Da Babu Kaffara, PDP Ce Za Ta Lashe Zabukan 2019 —Lamido Na Yi Rantsuwar Da Babu Kaffara, PDP Ce Za Ta Lashe Zabukan 2019 —Lamido Reviewed by Unknown on 9:54:00 AM Rating: 5

No comments:

(C) 2016 MBYBOX. Powered by Blogger.