ads

Sojoji sunyi jan kunne ga masu tada zaune tsaye



Zamu Yiwa Masu Tada Zaune Tsaye Ba Sani Ba Sabo - inji sojoji
Hedikwatar tsaron Nigeria ta gargadi daidaikun mutane da kungiyoyi da ke neman tada zaune tsaye da su guji wannan aika-aika ko kuma su yabawa aya zaki.

Rundunar tace ba zata lamunci duk wani yunkuri ko take-take na hargitsa zaman lafiyar kasar nan ba ta kowane irin suna.

Rundunar ta yi watsi da wani bidiyo da ake yadawa a kafafen internet cewa ba gaskiya bane. A saboda haka take kira ga jama'a da suyi watsi da shi.

"Dakarun mu sun dukufa ba dare ba rana domin dakile ayyukan ta'addanci da satar shanu da fasa bututun mai da garkuwa da mutane" inji Kakakin rundunar Janar Rabe Abubakar
Sojoji sunyi jan kunne ga masu tada zaune tsaye Sojoji sunyi jan kunne ga masu tada zaune tsaye Reviewed by Unknown on 9:18:00 AM Rating: 5

No comments:

(C) 2016 MBYBOX. Powered by Blogger.