ads

Zan yi bincike kan wutar lantarki — Buhari


Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce zai binciki gwamnatocin da suka gabata kan yadda suka tafiyar da harkokin wutar lantarkin kasar.
Shugaban ya bayyana haka ne a wata hira ta musamman da ya yi da gidajen talajibin da rediyo a Katsina a karshen mako.
Shugaba Buhari ya ce Najeriya ba za ta ci gaba ba idan dai ba a samu tsayayyiyar wutar lantarki ba, yana mai cewa dole ya yi bincike kan makudan kudaden da gwamnatocin da suka gabace shi suka kashe a fannin domin yin gyara mai dorewa.

Ya ce, "Dole ne mu yi bincike kan makudan kudaden da aka kashe a harkar wutar lantarki, ganin cewa duk da kudin da aka kashe ba a samun isasshiyar wutar. Matsalar ma'aikatar samar da hasken lantarki kamar matsalar ma'aikatar man fetur ce. An kashe fiye da $16bn amma babu tsayayyiyar wuta."
A baya dai tsohon shugaban kasar marigayi Umaru Musa 'Yar Adua ya zargi tsohon shugaban kasar Cif Olusegun Obasanjo da kashe fiye da $16bn domin samar da wutar lantarkin amma maimakon hakan kasar ta ci gaba da fama da matsalar rashin wutar.
Zan yi bincike kan wutar lantarki — Buhari Zan yi bincike kan wutar lantarki — Buhari Reviewed by Unknown on 3:48:00 PM Rating: 5

No comments:

(C) 2016 MBYBOX. Powered by Blogger.