ads

AN BAIWA HUKUMOMIN TSARON NIGERIA DAMAR MURKUSHE MASU NEMAN TADA ZAUNE



TSAYE Gwamnatin tarayyar Nigeria ta baiwa hukumomin tsaro damar su murkushe duk wani take-take na neman karya doka da Oda ko tada zaune tsaye a fadin kasar.
Wannan kiran ya fito ne daga Ministan tsaro na Nigeria, Mansur Muhammad Dan-Ali wanda ya bayyana haka yau Talata a wajen bude taron masu ruwa da tsaki kan sha'anin kafafen watsa labarai na rundunar tsaro.

Taron wanda kungiyar cibiyar bayar da bayanai kan sha'anin tsaro, Centre for Crisis Communication (CCC) tare da hadin guiwar hedikwatar tsaro ta Nigeria da kungiyar Nigeria Stability and Reconciliation Programme NSRP suka shirya ya gudana ne a Abuja.
Dan Ali yace Gwamnatin tarayya ba zata yi wasa da zaman lafiya da rayuka da dukiya da kuma walwalar yan Nigeria ba.
AN BAIWA HUKUMOMIN TSARON NIGERIA DAMAR MURKUSHE MASU NEMAN TADA ZAUNE AN BAIWA HUKUMOMIN TSARON NIGERIA DAMAR MURKUSHE MASU NEMAN TADA ZAUNE Reviewed by Unknown on 7:22:00 AM Rating: 5

No comments:

(C) 2016 MBYBOX. Powered by Blogger.