ads

Kungiyar Boko Haram Sun Fara Yin Amfani Da Dawakai Wajen Kai Hare-Hare




Hukumar Hedikwatar tsaron Nigeria tace yan kungiyar Boko Haram sun soma yin amfani da Dawakai wajen kai hare haren ta'addanci a kauyaku da garuruwan Arewa maso gabashin kasar
Kazalika rundunar tace mayakan na Boko Haram sun binne ababen fashewa a gonaki da nufin hallaka mutanen da basu ji ba basu gani ba
A saboda haka nema rundunar tsaron ta gargadi jama'a da suyi hattara da mutanen da suka gani a
dawakai ko wani kunshi a gonakin su

"jama'a su kai rahoton duk wani abu ko wasu gungun mutane da ba'a gane masu ba ga hukumomin tsaro domin daukar mataki kan lokaci" inji rundunar
Kungiyar Boko Haram Sun Fara Yin Amfani Da Dawakai Wajen Kai Hare-Hare Kungiyar Boko Haram Sun Fara Yin Amfani Da Dawakai Wajen Kai Hare-Hare Reviewed by Unknown on 6:54:00 AM Rating: 5

No comments:

(C) 2016 MBYBOX. Powered by Blogger.