ads

SOJOJIN RUWAN NIGERIA SUN KAMA MASU FASA BUTUTUN MAI SU 40 A DELTA


SOJOJIN RUWAN NIGERIA SUN KAMA MASU FASA BUTUTUN MAI SU 40 A DELTA
Rundunar sojin Nigeria, tace dakarunta sun tsaurara tsaro a hanyoyin ruwan kasar domin dakile ayyukan fasa kauri da satar mai da fasa bututu da fashi da makamai.
Sanarwar hakan ta fito ne daga Kakakin rundunar, Christian O. Ezekobe a yau Talata, inda yace wannan mataki umurni ne daga shugaban hafsan sojin ruwa Vice Admiral Ibok-Ete Ibas,

Yace kawo yanzu dakarun rundunar sun samu nasarar ganowa tare da lalata matatun mai na bogi a kauyen Lolomu da Tagola dake karamar hukumar Warri ta Kudu a jihar Delta.
Kazalika rundunar ta samu nasarar kama wasu mutane 40 masu haramtacciyar sana'ar fasa bututun mai a yankuna daban daban dake jihar da kuma wasu kayayyaki da suka hada da injinan fasa bututu da haramtattun mai.
SOJOJIN RUWAN NIGERIA SUN KAMA MASU FASA BUTUTUN MAI SU 40 A DELTA SOJOJIN RUWAN NIGERIA SUN KAMA MASU FASA BUTUTUN MAI SU 40 A DELTA Reviewed by Unknown on 6:36:00 AM Rating: 5

No comments:

(C) 2016 MBYBOX. Powered by Blogger.